Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni zai gana da jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya da yammacin yau Alhamis.
Jakadiyar Amurka Linda Thomas-Greenfield ta ziyarci Kampala babban birnin kasar kwanaki kadan bayan da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya kai ziyara birnin.
Da yake magana da kafar yada labarai ta BBC, Shugaba Museveni ya bayyana Ms Thomas-Greenfield a matsayin abokiyar kirki.
Da aka tambaye shi ko Ms Linda za ta kawo umarni daga Washington ne, shugaban ya bayyana karara cewa “babu wanda zai iya ba su umarni”.
Ana Tsaka Da Kangin Rayuwa Ka Bayar Da Kyautar N1.14BN Ka Gaggauta Dawo Da Su – SERAP Ga Buhari
Sai dai shugaban ya ce, ba bu wani yunkuri na sauya matsayar kasar kan yakin Ukraine. Domin kuwa Uganda na daga cikin kasashen Afirka 16 da suka kaurace wa kudurin Majalisar Dinkin Duniya na neman Rasha ta dakatar da mamayar da takewa Ukraine
Da aka tambaye shi matsayinsa kan rikicin, Shugaba Museveni ya yi kwatancen rikicin da irin makami mai linzami na Cuba da aka harba tun a shekarar 1962.
Ya danganta kasancewar Nato a gabashin Turai da yunkurin da Tarayyar Soviet ta yi na harba makaman nukiliya a Cuba, mai nisan mil daga gabar tekun Florida.
Shugaba Museveni ya ce Uganda ta goyi bayan Amurka ta fuskar tsokana a lokacin, kuma ya kamata a yi amfani da irin wadannan ka’idoji a yau.
Kazalika Shugaban ya kara da cewa ya fahimci irin ayyukan da Rasha ke yi a Ukraine da kuma abin da mutane ke kira tarihi, lamarin da kuma ya kira shi da al’amuran yau da kullun.