Shugaban Sabuwar Ƙungiyar Kwallon Kafar Nahiyar Turai ta European Super League Florentino Perez, ya ce babu wanda ya isa ya kori Kungiyoyin Kwallon Kafa ta Chelsea da Manchester City da Real Madrid daga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta wannan kakak ko da baan sun balle daga gasar.
Perez wanda shine shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya ce kazalika babu wanda ya isa ya hana yan wasan Wakiltar ƙasashen su a gasar cin kofin duniya wai don sun balle daga gasar zakarun nahiyar turai.
Dukkanin wadannan barazana sun fito ne daga Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar turai wato UEFA bayan da ta ayyana sunayen wasu kungiyoyi sha biyu dake shirin ballewa daga gasar su kirkiro tasu ta European Super League.
A Yanzu haka dai gasar da ake shirin bude ta nan gaba kaɗan, ta ƙunshi kungiyoyi sha biyu da suka hada da AC Milan da Arsenal da Atletico Madrid da Barcelona da Chelsea da Inter Milan.
Sauran sun hada da Juventus da Liverpool da Manchester City da Manchester United da Real Madrid gami da Kungiyar Tottenham, kuma suna ta ƙoƙarin kara kungiyoyi uku cikin gasar.
Hukumar UEFA ta nuna fushin ta matuƙa kan Wannan mataki na ballewa, inda ta ce duk Ƙungiyar da ta kuskura ta balle kuma tana cikin gasar zakarun turai na bana to lallai zata yi da na sani.
Kungiyoyin Chelsea da Manchester City da Real Madrid dukkannin su sun tsallaka zuwa wasan kusa da karshe na Champions League, yayin da Arsenal da Manchester United kuma sun tsallaka zuwa zagayen kusa da karshe a gast Europa.
To sai dai Perez ya ce babu wanda ya isa ya kore su saboda doka ba ta bada damar hakan ba