Gwamnan Jahar Gombe Mohammed Inuwa Yahaya yace ko shi ko Sanata Ɗanjuma Goje, babu wanda yasan ko zai rayu har zuwa shekarar 2023.
Gwamnan ya bayyana haka a ranar Talata a lokacin da yake amsa tambaya daga Manema labaru a Fadar Shugaban Ƙasa dake Villa, Abuja.
Idan dai ba’a manta ba, a ranar Juma’a wasu ɓata gari suka kai hari a tawagar Sanata Mai Wakiltar Gombe ta tsakiya, a lokacin da zai je Babban Birnin Jahar domin halartar ɗaurin Aure.

KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Anambra: Anyi Batakashi Tsakanin Yan Sanda Da Yan Kungiyar IPOB A Ihiala Har Na Tsawon Awa 3
Mai Taimakawa Tsohon Gwamnan Jahar ta Gombe Lilian Nworie, a cikin sanarwar daya fita, yayi zargin cewa ɓata garin da suka kai harin, sun kasance masu biyayya ga Gwamnan Jahar Gombe Yahaya, bayan an samu hatsaniya tsakanin sa da Sanata maici a yanzu.
Goje, wanda yakai ƙara ga Attoni-Janar na Ƙasa Abubakar Malami ya buƙaci ayi bincike akan wanda suka kai mashi harin, wanda a dai-dai lokacin ya sanar da Sufeto-Janar na Ƴan sandan Ƙasar nan Alƙali Baba, sa Shugaban Hukumar Kula da Ƴan sanda, da Ministan Ƴan sanda, gami da Kwamishinan Ƴan Sanda.
A lokacin da yake jawabi a ranar Talata, Gwamnan Yahaya, yasha alwashin kawo ƙarshen ayyukan ƴan Ƙungiyar Kalara, yana mai gargaɗi ga duk wanda ke tarayya dasu, daya daina.
Akan ƙalubale da yayi cewa, wasu jami’an Gwamnatin Jahar Gombe na gargaɗin ɗaukar rayuwar shi, Gwamnan yace bincike zai nuna gaskiyar lamari.
Gwamnan wanda aka tambaya cewa, ko faɗa su nada nasaba da sake zaɓen shi a shekarar 2023, yace Allah kaɗai yasan cewa ko shi ko Goje wani zai kai 2023.