A wani sako da Fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter, ta yi watsi da rahotannin da wasu kafafen watsa labarai suka bayar cewa wani hadimin shugaban kasar ya kamu da cutar korona.
Fadar shugaban kasar ta ce dukkan hadiman shugaban kasar suna yin gwajin cutar ta korona kuma hadimin da aka ce ya kamu da cutar bai kamu da ita ba.
Inda suka shawarci al’umma da su yi watsi da wadannan labarai wadanda aka kitsa domin a kawar da hankalin mutane sannan a sanya fargaba a game da lafiyar shugaban kasa.
Cutar ta korona ce ta yi ajalin shugaban ma’aikatan fadar Shugaba Buhari, Malam Abba Kyari.