Hukumar kula da kadarorin gwamnati da tsaron al’umma NSCDC, ta kafa wani kwamiti da zai gaggauta bin diddigin biyan alawus-alawus na ma’aikatan da suka gudanar da zaben Osun da Ekiti a shekarar 2022.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Mista Olusola Odumosu, daraktan hulda da jama’a na NSCDC, ya bayyana haka a ranar Alhamis a Abuja cewa, gwamnatin tarayya ta saki kudaden domin a biyan kudin.
KARANTA KUMA Shugaban Kasa Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Jami’an Hukumar NSCDC
“Kwanan nan ne gwamnatin tarayya ta saki alawus-alawus din zaben jihar Osun wanda ake ci gaba da biyan ma’aikatan da suka shiga aikin zaben.
“An kuma yi mana alkawarin cewa kudaden alawus-alawus na zaben Ekiti na kan shirin mika wa ma’aikatan.
“Saboda haka ana kira ga ma’aikatan da suka damu da su kara hakuri saboda ba za a iya kammala aikin biyan kudin a rana daya,” in ji shi.
A cewar Odumosu, asusun da aka saki kudin kwanan nan ya faru ne saboda jajircewa da kuma kishin Kwamandan NSCDC, Ahmed Audi, ana ganin ba a mayar da jin dadin ma’aikatan ba.
“CG yana matukar sha’awar jin dadin ma’aikata kuma ba zai nannade hannunsa ya bar ma’aikatan su yi bacin rai ba, wahala ko kuma rashin tausayi a yayin gudanar da ayyukansu musamman a babban zabe mai zuwa.” Odumosu ya nanata.
Ya bayyana cewa, don gaggauta biyan kudin, CG ya kafa wani kwamiti bincike, karkashin jagorancin Daraktar kudi da asusu, Misis Comfort Danladi.
A cewarsa, kwamitin zai bi diddigin ma’aikatar kudi ta tarayya domin ganin an fitar da dukkan kudaden.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa, Odumosu ya musanta rahotannin shirin da wasu NSCDC suka yi na kin shiga zabe mai zuwa.
“Za a tura dubbannan jami’an NSCDC zuwa kowane lungu da sako domin gudanar da zaben da kuma kare muhimman ababen more rayuwa na kasa.
A Wani Labarin Kuma Kotu Ta Aike Da Shahararriyar ‘Yar TikTok Murja Kunya Zuwa Gidan Kurkuku
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hoki a Kano, ta tasa keyar wata fitacciyar ‘yar TikTok Murja Ibrahim Kunya a gidan gyaran hali bisa zargin ta da aikata laifukan da suka saba wa koyarwar addinin Musulunci da kuma yi wa mutane barazana a Tiktok.
Murja ta bayyana a gaban kotun da Abdullahi Halliru ke jagoranta bisa wasu tuhume-tuhume guda biyu da suka hada da barazanar kai hari ga wasu mutane da kuma fitar da bidiyoyi masu tayar da hankali da suka saba wa ka’ida da koyarwar addinin Musulunci, wanda hakan na iya jawo wasu kuskure.