Ministan yada labarai da al’adu, Mista Lai Muhammad, ya bayyana cewa babu wani shirin da gwamnatin Shugaban Kasa Buhari ta yi a halin yanzu na ruguza majalisar zartarwa ta tarayya. A makon da ya gabata ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umurci dukkan ministocinsa da su kawo cikakken rahoton ayukkan hukomomi da ma’aikatunsu suka aiwatar a karkashinsu. Buharin, ya umurce su da su mika rahoton nasu ga ofishin sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha. Wannan umurnin na Buhari, ya jawo maganganu da hasashen cewa, shugaban kasar na shirin sauya ‘yan majalisar zartarwarsa ne kafin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu nan mai kamawa a karo na biyu. Da yake bayani ga ‘yan jarida da ke fadar shugaban kasa ranar Alhamis jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya, Mista Lai ya bayyana cewa, “Mukarabban Gwamnati na nan lafiya, babu wani abu da ya same su. A ranar 22 ga watan Mayu za mu yi zaman karshen wa’adin mulki na farko,” in ji shi. Bayanan na Ministan Labarai sun taka wa masu yada ruguza majalisar zartarwar kwanan birki.