Shuwagabancin Jami’ar Lagos ta bayyana wani rahoto (ba wanda Dimokuraɗiyya ta fitar ba) akan yunƙurin sace mutane a cikin Jami’ar a matsayin ƙarya.
Wasu masu amfani da yanar gizo sun ɗora wani bidiyo, suna masu cewa an kama wasu masu tsafi a ƙofa ta biyu ta UNILAG a yayinda aka ga suna ƙoƙarin sace ɗaliba mace.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Wakilai Ta Bada Shawarar Kwastam Ta Biya Diyyar Naira Miliyan 360 Kan Kashe-kashen Da Aka Yi
Amma Shuwagabancin Makarantar, a cikin wata sanarwa, tace abun da aka gani ba gaskiya bane.
“Lamarin ya faru ne tsakanin ƙoƙarin yin ba dai-dai ga ɗalubai, a yayinda wani yayi yunƙurin guduwa daga hannun Jami’an tsaro a bakin ƙofar. Lamarin an tura shi a ɓangaren Tsaro da harkokin Ɗalibai na Jahar.
Shugaban Jami’ar da Shuwagabancin Jami’a ya bayar da tabbacin ga ɗalubai, iyaye da Al’umma cewa tsaron Sojoji shine abinda suka baiwa fifiko a Jami’ar Lagos,” inji sanarwar Jami’ar.
Shima Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Lagos Adekunle Ajisebutu ya tabbatar da cewa lamarin karya doka ne, bawai ƙoƙarin satar mutane a Makarantar..