Wani malamin Majami’a a Najeriya ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta na zamani, bayan wata fatawa da ya kawo dake nuni da cewa ko da namiji ya aikata zunubi a yanzu, to babu abinda zai kai shi wuta.
Da yake wa’azi a yayin taron ibada da aka gudanar a wani coci, Malamin Majami’ar ya ce Yesu Almasihu ya riga da ya mutu da zunuban kowane Namiji a duniyar nan don haka babu wani zunubi kuma a kan maza.
Cikin wani faifan bidiyo dake ta karakaina a shafukan intanet, an ji yadda malamin Majami’ar ke faɗa da kakkausar murya cewa babu wani zunubi da zai sake hawa kan namiji a wannan duniya da muke ciki.
Malamin Majami’ar da ba a bayyana sunansa ba, ya ce Yesu Almasihu ya mutu ne a radin kansa don kankare wa mutane zunubansu, ba wai don wani abu ba.
A Najeriya irin wannan fatawa ba bako ba ne a wurin malaman addinin Kirista, inda ko a baya ma an samu wani dake nuni da cewa shan magani ba dole ba ne ga maras lafiya.