Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a Jihar Legas ranar Asabar ta karyata rahotannin damke jami’anta bisa zargin kafa wata cibiyar tantance masu kada kuri’a ba bisa ka’ida ba.
Kwamishinan zabe na INEC a jihar Legas Mista Olusegun Agbaje ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matasa Ne Musamman ‘Yan Mata Zasu Tantance Zaben Badi – Shugabar Matan Jam’iyyar APC
NAN ya tuna cewa wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa jami’an ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda da ke Ijeshatedo sun kama wasu jami’an INEC guda uku a jihar bisa zargin su da hada baki da cocin St. Brigigs Catholic, Ijeshatedo, Legas, wajen kirkiro tare da kuma cigaba da yin rajistar masu kada kuri’a ba bisa ka’ida ba ta CVR a cikin coci.
Da yake mayar da martani Agbaje ya bayyana rahoton a matsayin labaran karya.
“Dukkan ma’aikatana da injina sun cika. Babu wani ma’aikacin INEC da aka kama a ko’ina a fadin Legas ranar Juma’a,” in ji REC.
Idan zaku iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa INEC a ranar Juma’a, ta musanta rahotannin mamaye cibiyar ta CVR da wasu ‘yan daba suka yi tare da kwashe na’urorinta na rajista.
An sami karuwa sosai a yawancin cibiyoyin rajistar masu jefa kuri’a a cikin jihar gabanin wa’adin ranar 31 ga watab Yuli.
NAN