Babu wata Gwamnati data saki kuɗaɗe domin Inganta Jami’o’in Gwamnati ba tare da ƙoƙarin mu ba — ASUU
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta bayyana cewar babu wata Gwamnati data saki kuɗaɗen domin inganta Jami’o’in Gwamnati ba tare da ƙoƙarin da Gwamnatin take yi ba.
Ƙungiyar ta bayyana haka a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zargin Magudi: Yan takarar gwamna uku na jam’iyyar PDP a Zamfara sun janye daga zaben fidda gwani
Ƙungiyar ASUU tace idan ƙungiyar ta kasa yin wani ƙoƙari domin samar da tsarin Jami’o’i mai kyau, makomar ƙasar zai ɓaci.
Shugaban Ƙungiyar reshen Jami’ar Ibadan Farfesa Ayo Akinwole a lokacin da yake jawabi a gidan talabijin na Oyo, ya jaddada cewa babu wata Gwamnati data saki kuɗi don raɗin kanta ga Jami’o’i ba tare da shiga Yajin aiki ba.
Akinwole yayi kira ga ƴan Najeriya da kada su zama masu goyon bayan Gwamnatin Tarayya akan ƙarin Albashi da aka yi masu.
Akinwole ya bayyana cewar abun baƙin ciki ne yadda Gwamnatin Tarayya ke son ganin ta gaya wa mutane wasu jawabai yanda zasu tsani Ƙungiya, kuma har yanzu bata maida jawabi akan abubuwan da ASUU ke buƙata.
Yace Yajin Aikin yanzu na gaba ɗaya.