Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari a ranar Juma’a yayi ɓaɓatun cewa, babu wata gwamnati tun bayan dawowar Dimokuraɗiyyar a shekarar 1999 data yi abinda yayi a shekaru 6 na mulkin sa.
Buhari ya bayyana haka a jawabin da ya yiwa ƙasar domin murnar cikar Najeriya 61.
Tsofaffin shugaban ƙasa da suka haɗa da Olusegun Obasanjo, da Umaru Musa Yar’adua, da Goodluck Jonathan sune waɗanda suka gabace shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamu tabbatar mun tsamo ƴan Najeriya Miliyan 10 daga ƙangin talauci a shekaru 10 masu zuwa — Buhari
Buhari yace ya cimma nasarori da dama a shekaru shida da suka gabata a ƙarƙashin mulkin sa.
Yace masu caccakar sa, suke kawo tsaiko, kuma basa iya ganin ɗimbin nasarorin da aka cimmawa.
“Tun hawan mulkin wannan gwamnatin, ta magance matsaloli da dama, duk da matsin tattalin arziki.
“Babu wata gwamnati tun shekarar 1999 da tayi abinda nayi a shekaru shida, wanda an dawo da Nigeria a hanya madaidaiciya.
“Zamu cigaba da yiwa ƙasar mu aiki, saurare gami da kare tsarin Dimokuraɗiyya,” inji shugaban ƙasa.
To Allah ya gani inhakane to alummar Nigeria xasuyine alkalacin
Shugabani Koji tsoro Allah atina alummar Nigeria
muhammadumamuda689@gmail.com tudun nufawa kano Municipal local government
malam muhammadu buahari kenan a nigeria