Mista Moyo Ogunlewe, Shugaban Karamar Hukumar Kosofe ta Jihar Legas, ya ce babu wata kasa mai hankali da za ta yi watsi da saka hannun jari a harkar ilimi saboda a cewarsa har yanzu bangaren na da gudummawa babba da yake bayarwa wajen bada damarmaki.
Ogunlewe ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake rarraba fom din Jarabawar GCE guda 150 ga dalibai marasa galihu a yankin karamar hukumar.
A cewarsa, gwamnatinsa tana aiwatar da manufofin ilimin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar domin inganta yanayin rayuwa.
Ogunlewe ya ce lokacin da mutane suka fi ilimi, za su iya magance matsaloli da kyau.
“Wannan yana nufin cewa al’umma na iya samun ci gaba cikin sauri.
“Mutanen da ke da ilimi za su iya fahimtar tarihin al’ummarsu da yanayin tattalin arzikinta na yanzu. Don haka, suna iya karkata ga shiga siyasa da inganta kasarsu.
“Ilimi da hazaka ba na masu hannu da shuni ne kadai ba. Ilimi kyauta yana faɗaɗa ƙofar dama ga kowane yaro, musamman waɗanda aka dakile baiwar su saboda talauci, ”in ji shi.
Ya ce tare da son siyasa da jagoranci mai kyau gwamnati na iya taimakawa wajen samar da al’umma dama da karfafawa ga kowane dan kasa.
“Na san cewa babu wata hanya mafi kyau don yin hakan, amma ta hanyar samun ilimi. Duk ƙasar da ke da niyyar sauya kanta zuwa mai inganci domin tafiya daidai da zamani a cikin bukatar duniya dole ne ta sami ingantattun manufofin ilimi.
“Shugabanci zabi ne- Na zabi na saka hannun jari a nan gaba ga matasan mu. Mun yanke shawarar amfani da kudaden da muke samu daga albarkatun mu domin taimakawa bangaren ilimantar da matasa domin fitar da sauyin tattalin arzikin mu.