Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya bayyana bacin ransa game da yadda ‘yan ta’adda suke ta kashe mutane a jihar, gwamnan yace babu wata sauran yarjejeniya da ta rage tsakaninsa da ‘yan ta’addan.
Masari yace ‘yan ta’addan sun saka hannu a yarjejeniyar da suka yi da gwamnatin cewa sun tuba ba zasu kara aikata laifukan da suka yi ba, sai dai basu cika alkawarin da suka dauka ba.
Masari ya bayyana haka ne a yayin da ya tattaunawa da BBC ta faifan bidiyon kai-tsaye na shafin Instagram inda yace, “basu cika alkawari ba, kuma sun yaudare mu”.
Ya kara da cewa wasu daga cikin ‘yan bindigar daga jihar Zamfara, Kaduna da kuma jamhuriyar Nijar suke.
https://dimokuradiyya.com.ng/taaddanci-yan-bindiga-sun-kashe-hakimi-a-jihar-katsina/
Masari yace, shi ne gwamna na farko da ya fara yin sulhu da ‘yan bindigar a shekara ta 2016, domin baya so a ce an samu salwantar rayuka amma duk da hakan basu martaba alkawarin da suka yi ba.
“Saboda mu martba alkawarin da muka dauka, muka dakatar da ‘yan Kato-da-gora da kuma ‘yan agajin sa kai, saboda mu basu dama su yi rayuwarsu cikin walwala”.
Gwamnan yace wasu daga cikin ‘yan bindigar su kan kai hari har akan dabobbi ba wai iya kan mutane suka tsaya ba.
Gwamnan ya kara da cewa daga cikin jami’an dake yaki da ‘yan ta’addan akwai sojin saman kasar nan, kuma sun samu nasarori da dama, sai dai yana kira ga gwamnatin tarayya kan cewa sojin suna bukatar kayan aikin da ya kamata.