Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ƙaryata maganganun da jama’a ke yi na cewa gwamnatinsa ta ja layi wa wata kafar Talabijin ta Yanar gizo daga daukar rahotannin harkokin gwamnatin tasa.
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Sadarwa ta Jihar Yusuf Idris Gusau ya sanya wa hannu, ta ce jama’ar da suka kago labarin, sun yi ne da zummar shafa wa gwamnatin Matawalle Kashin Kaji.
Sanarwar ya ce ko da yake gwamnatin tarayya ta ta ja layi kan duk wasu masu yaɗa labaran bogi, to amma har yanzu akwai daidaikun kafafen dake ci gana da cin laren su babu babbaka.
To sai dai ya ce babu makawa gwamnati za ta yi maganin duk mai hannu a irin haka, domin gujewa tada zaune tsaye.