Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya karyata batun cewa akwai bangaren da ‘yan bindiga ne ke da iko da su a jihar ta Sakkwato.
A cewarsa, labarin karya ne, wadanda ba su taba son gwamnatinsa bane ke yayata batun. Ya ce sam ba ya adawa da masu caccakar gwamnatinsa musamman wadanda suke son a kawo gyara, amma abin da yake cewa shi ne; mutane su tabbatar da ingancin bayanansu kafin su bayyanawa al’umma.
Gwamnan ya ce wadansu kungiya sun yi taron ‘yan jarida kwanan nan sun yi zargin cewa akwai wadansu bangare a jihar Sakkwato da al’ummar yankin sai sun nemi izinin ‘yan bindiga suke iya zuwa kasuwa ko yin taron biki. Inda Gwamnan ya ce; “Bayan na ji labarin sai na kira Daraktan DSS akan ya kira jagoran wannan kungiya ya tambaye shi cikin ruwan sanyi ya bayyana masa wadannan wuraren domin daukar matakin ‘yanto wuraren, amma bayan ya zo, sai ya ce shima an yi masa karya ne, sai ya bada hakuri bisa hakan.” Inji gwamnan.