Wani mutum da ba a bayyana sunan sa ba, ya cinna wa gidansa wuta da gangan a jihar Kwara, kamar yadda jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka bayyana.
Mista Hassan Adekunle, wanda shi ne kakakin daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Falade Olumuyiwa, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:28 na safiyar jiya Lahadi a yankin Lekki Phase One da ke unguwar Eyenkorin a Ilorin, babban birnin jihar.
Adekunle, yayin da yake zantawa da manema labarai ya ce mutumin ya yi ikirarin cewa da gangan ya fesa ma gidan mai mai dakuna uku tare da cinna masa wuta saboda tsananin takaicin matarsa.
A cewarsa, gobarar ta iya kone gidan kurmus, amma wani mazaunin yankin da ya yi gaggawar sanar da hukumar kashe gobara game da lamarin ya taimaka wajan saukaka lamarin..
Adekunle ya kara da cewa, daukin gaggawar da jami’an hukumar kashe gobara suka kai ne ya sa aka shawo kan gobarar tare da hana ta yaduwa zuwa wasu sassan gine-ginen yankin.
Olumuyiwa, a nasa jawabin, ya yi kira ga mazauna jihar da su kara sanya ido ga gidajensu, ofisoshinsu, da kuma duk inda suka samu kansu.
A wani labarin kuma na daban
A hukumance an ayyana bullar cutar Ebola ta baya-bayan nan a Kongo, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a ranar Litinin din nan.
Hukumad ta ce barkewar cutar ta shafi lardin Equateur da ke arewa maso yammacin kasar, inda aka samu bullar cutar ta farko a ranar 23 ga Afrilu.
Ya ce a cikin dukka, an tabbatar da kamuwa da cutar mutane guda hudu da kuma mutum daya da ake zargi da kamuwa da cutar, amma majinyatan duk sun mutu ne sanadiyyar cutar.
A wata barkewar da ta gabata a lardin tsakanin Yuni zuwa Nuwamba 2020, an gano jimillar mutane 130 kuma mutane 55 sun mutu.
Koyaya, barkewar sabuwar cutar ita ce ta 14 da aka rawaito a cikin ƙasar mai mutane miliyan 90 tun 1976.
A tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016, cutar ta barke a mafi girman garuruwa a yammacin Afirka inda sama da mutane 11,000 suka mutu.
Cutar Ebola takan haifar da zazzabi mai zafi da zubar jini a cikin jikk, kuma tana yin barazana ga rayuwa. (dpa/NAN)