Makusancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Air Commodore Umar Mohammed Mai ritaya a ranar Juma’a, Babbar Kotun Tarayya dake Abuja sakamakon zargin sa da badaƙalar kuɗi har Dala $1.03 da Gwamnatin Tarayya ta kaishi ƙara.
Mai Shari’a Inyang Ekwo a hukuncin daya yanke yace Gwamnatin Tarayya bata da hujjoji akan Mohammed da kamfanin sa Easy Jet Integrated Services Ltd kamar yadda doka ta tanada.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Jihar Kwara Ya Rantsar Da Sabbin Mambobin Majalisar Ministoci, Ya Kuma Yi Wa Wasu Uku Garambawul
Ofishin Antoni-Janar ta kama Mohammed, wani mamba a kwamitin Shugaban ƙasa akan tsaro da kamfanin sa, ta zarge shi da badaƙalar kuɗi da mallakar bindiga ba bisa ƙai’ida.
A lokacin shigar da ƙarar Mohammed da kamfanin sa Easy Jet an kama shi da almundahanar Dala $1,030,000.
Dayake yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai Shari’a Ekwo ya bayyana cewar bawai Gwamnatin Tarayya ta kasa bada hujjoji, ta kasa bada hujjoji da zasu tabbatar cewa ya cinye Dala $1,030,000.
Comments 1