Bada jimawa ba zamu kawo karshen ta’adancin a Najeriya
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa nan da dan lokaci kada. Najeriya zatai maganin ta’addanci dake aukuwa a kasar.
KARANTA:-Yadda na kashe ma’aikacin gidan Super Tv
A lokacin da yake tarbar mai girma Sarkin Ekiti Oba Adeola Ajakaiye jiya a Abuja yake cewa Yan Najeriya su bada hadin kansu ga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman Lafiya a Najeriya.
Yace ina mai tabbatar muku nan da lokaci kadan maganar rashin tsaro zai zama tarihi za’a koma zaman Lafiya da kwanciyar hankali a kasa.
Yace shugaban kasa ya tanadi wani kwamiti wanda zai dogon nazari kan lamarin tsaro tare da kawo sauyi da gyara kan lamarin sojoji da Yan sanda da sauran jami’an tsaro.
Osinbajo ya kara jawo hankalin sarakuna da gwamnatocin jaha da kansiloli dasu hada kai da gwamnatin tarayya don magance matsalar tsaro.
Yake cewa kasa irin wannan mai cike da matsaloli na rashin tsaro nada bukatar hadin kan kowane sashi don ganin an kawo karshen wannan ta’adancin dake kasar.
Yace gwamnatin tarayya na matukar damuwa kan lamarin tsaro kuma tana bukatar hadin kan kowane sashi don ganin an kawo karshen ta’adancin dake kasar.
Ya bayyana jindadinsa kan irin yadda bakonsa ya kaddamar da wani kwamiti a yankinsa don ganin an kawo karshen rashin tsoro a yankin.
Osinbajo ya kara da cewa gwamnatin tarayya zata bada gudummawa ga wannan kwamiti don cinma manufarta na dakile ta’addanci.
Comments 1