dariya

Nishadi: Bafulatani Da Professor

Daga Sulaiman Umar AC

Profesa yace idan nayi maka tambaya baka amsa ba zaka bani 5000. Idan kuma kayi min tambaya bansaniba zan baka 20000. professor ya tambayi bafulatani “nawa ne nisan sama zuwa kasa?” Bafulatani yace bai sani ba.
Bafulatani ya ba da 5000. Bafulatani yace saura ni.”Wace dabba ce idan tana kasa tana da kafa 4 idan ta soma tashi tana da kafa 3 idan tayi sama sai ta koma kafa 2 idan ta tashi saukowa sai ta sauko da kafa 1?” Profesa ya zaro 20000 ya bayar dan bai sani ba. Bafulatani zai tafi sai profesa yace “menene ansar?”. sai bafulatani ya zaro 5000 ya karawa profesa yace NIMA BAN SANI BA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *