Gwamnan Jahar Kebbi Abubakar Bagudu ya amince da fitar da Naira biliyan shida domin biyan kuɗaɗen garatuti ga Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi na Jahar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa akan Kafafen Yaɗa Labaru Yahya Sarki ya fitar, aka rarraba wa Manema Labaru a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC Ta Tsayar Da Ranar 26 Ga Fabrairu Domin Gudanar Da Zabukan Maye Gurbi 6, Ta Gargadi Jam’iyyu
A cewar Sanarwar, Ma’aikatan da suka ajiye aiki daga shekarar 2017 zuwa 2018, kuma suka karɓi rabin kuɗaɗen sallamar su, za’a biya su sauran kuɗaɗen su.
Sanarwar ta ƙara dacewa “suma waɗanda suka ajiye aiki daga shekarar 2019 zuwa 2020 da kuma 2021 suma zasu karɓi sauran kuɗaɗen su.”