An dawo da wani rukunin mutane na ‘yan Najeriya guda 167 da suka fake a kasar Libya zuwa gida.
Sun isa kasar ne da yammacin ranar Talata a filin jirgin saman Murtala Muhammad (MMIA), dake jihar Legas.
Wadanda aka dawo da su sun hada da manya mata 65, yara mata takwas, manya maza 76 da yara maza 18.
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Alhaji Mustapha Habib, wanda ya karbe su, ya shawarci matasan da gujewa zaman butulci a kasashen waje.
Shugaban wanda ya samu wakilcin kodinetan ofishin hukumar NEMA a Legas, Ibrahim Farinloye, ya bukaci wadanda suka dawo da su zauna cikin Gida Najeriya, domin yin amfani da dimbin albarkatu masu yawa da kasar ta mallaka.