Gareth Bale ba zai samu fafatawa a wasan farko na gasar zakarun nahiyar Turai na wannan kaka da za a gwabza tsakanin kungiyarsa Real Madrid da Inter Milan ba.
Bale bai samu shiga fafatawar da Madrid ta lallasa Celta Vigo da ci 5-2 a ranar Lahadi ba bayan da ya ji rauni a yayin atisaye.
Rahotanni sun ce Bale zai yi jinya ne har zuwa watan Oktoba, saboda haka ba zai samu doka wasanni biyu na gasar zakarun nahiyar Turai ba, da kuma na La Liga har 4.
A wannan watan dan wasan gaban na Wales ya jefa kwallaye 3 rigis a ragar Belarus har gida, a wasan neman cancantar fafatawa a gasar cin kofin duniya, kuma ya fafata wa Wales a wasan da suka buga canjaras da Estonia ranar Laraba.
Bale, wanda yake cikin shekarar karshe na kwantiraginsa da Real Madrid, ya kwashe kakar da ta gabata a Tottenham a matsayin aro, kuma yanzu da ya dawo ya buga wa Madrid wasannin La Liga 3, kuma ya ci kwallao a canjaras 3-3 da suka buga da Levante.