Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa harin da aka kai hedikwatar ‘yan sanda a birnin Owerri ta jihar da kuma kurkukun garin harin ta’addanci ne, kuma ya bayar da umurni da dukkan bangarorin jami’an tsaron jihar Imo, su bazama domin nemo “ƴan ta’addan” da suka ɓalla kurkuku da far wa hedikwatar ‘yan sandan jihar a ranar Litinin.
Shugaba Buharin ya kuma yi Allah-wadai da harin tare da cewa na ta’addanci. Wannan na kunshe cikin sanarwar da maitaimaka masa kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Sanarwar ta kara da cewa lallai jami’an tsaro su tabbatar sun kamo ‘yan bindigar tare da hukunta su yadda doka ta tanada.