Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 21 suka jikkata, sakamakon fashewar wasu bama-bamai a Afganistan a yau Asabar.
Wannan shine karo na farko tun bayan da sojojin Amurka suka bar kasar a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2021, yayin da kuma kungiyar Taliban ta kafa mulkin rikon kwarya a kasar.
A cewar majiyoyi dake fitowar daga Kasar, fashewar abubuwa uku, sun faru ne daya bayan daya a birnin Jalalabad da ke gabashin kasar, da kuma wani a Kabul babban birnin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa, Mutane biyu sun mutu sakamakon fashewar bama -baman, a cewar wani asibitin gwamnati dake Jalalabad, yayin da wasu 19, da suka hada da yan Kungiyar Taliban suka jikkata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun farmaki Tangaza a Sokoto, Sun Debi kayan abinci
Tunda fari Wata motar yan kungiyar Taliban ce aka yi niyyar tarwatsawa a yankin Angorbagh, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, kamar yadda wani ganau ya shaida wa manema labarai.
“Mutane biyu sun jikkata sakamakon fashewar wani abu kafin azahar a unguwar Dasht-e-Barchi na Kabul” a cewar majiyar,
Sai harkawo hada wannan rahoton Kungiyar Taliban ba ta ce komai ba, game da asarar rayuka da akayi sanadiyar wannan mummunan harin.
Duk da cewa babu wanda ya dauki alhakin kai wadannan hare-hare kawo yanzu, ana zargin kungiyar ISIS na da alaka da harin, domin kungiyoyin biyu sun kwashe shekaru suna gwamza kazamin fada da juna.
A wani labarin Kuma makamancin wannan
A yau Asabar, an haramta wa yan mata komawa makarantun sakandare a Afghanistan, bayan sabbin shugabannin Taliban na kasar sun ba da umarnin samari da malamai maza ne kawai za su koma aji domin karatu.
Kungiyar masu tsatsauran ra’ayin Islama ta kori gwamnatin da Amurka ke marawa baya a watan da ya gabata, inda ta yi alkawarin yin mulki mai sassauci fiye da mulkinsu na tsatstsauran ra’ayi a shekarun 1990, lokacin da aka haramta wa mata yawan karatu da aiki.
Amma sabon sanarwar da ta fito daga ma’aikatar ilimin kasar, ta kasan ce sabon yunƙurin daga sabuwar gwamnati na Taliban, na yin barazana ga tauye hakkokin hakkin mata.
Sanarwar ta ce “Duk malamai maza da ɗalibai ya kamata su halarci Makarantun su,” inji wata sanarwa daga Taliban, kafin fara karatun a yau Asabar.
Sanarwar, wacce aka fitar da ita cikin daren jiya Juma’a, ba ta lamunce wa malamai ko dalibai mata koma wa makarantu ba.
Sai dai idan za’a iya tunawa tun bayan barkewar cutar Corona a kasar, Makarantun sakandare, da suka kunshi dalibai masu shekaru tsakanin 13 zuwa 18, galibi ana rarrabe su bisa dubi da jinsi a Afghanistan.
Comments 1