Wasu fashe fashe guda biyu sun afku a Kampala babban birnin kasar Uganda a ranar Talata, inda suka kashe akalla fararen hula uku, a wani harin da ‘yan sanda suka bayyana a matsayin wani harin hadaka na masu tsatsauran ra’ayi masu adawa da gwamnati.
Yan kunar bakin wake uku kuma sun mutu a tashin bama-baman, in ji ‘yan sandan kasar
Fashewar sun haifar da hargitsi a Kampala yayin da mazauna birnin suka firgita suka tsere daga tsakiyar birnin.
Kakakin ‘yan sandan Fred Enanga ya ce “har yanzu barazanar bama-bamai tana ci gaba da tashi, musamman daga ‘yan kunar bakin wake,” in ji kakakin ‘yan sanda Fred Enanga, yana mai dora alhakin fashewar a kan Allied Democratic Forces, wata kungiyar masu tsattsauran ra’ayin Islama.”
Tagwayen fashewar sun faru ne cikin mintuna uku tsakanin da juna. Dukkansu dai maharan ne dauke da ababen fashewa suka Kai harin.
Enanga ya ce, ‘yan sandan sun bi su tare da kwace makamai daga wani hari da ake zargin dan kunar bakin wake ne yayi yunkurin Kai wa, inda daga bisani jami’an suka yi nasarar dakile harin na uku.
‘Yan sanda sun fitar da faifan bidiyo na jami’an tsaro a daidai lokacin da ‘yan kunar bakin wake suka tayar da na’urorinsu a kan tituna, lamarin da ya sanya gizagizai ya turnuke da hayaki