Ma’aikatan bankunan kasuwanci a kasar nan sun tunkari babban bankin Kasa (CBN) kan ikirarin cewa bankunan na da isassun kudade na naira a cikin rubunsu amma suna tarawa.
Bankunan sun yi tir da babban bankin na CBN ne a lokacin da jami’ansu suka bayyana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken karancin sabbin takardun kudi da kuma wa’adin da babban bankin ya bayar a ranar 31 ga watan Janairu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Misis Hadiza Ambursa, jami’ar bankin Access Bank, wacce ta wakilci Manajan Darakta na bankin ta ce kashi 10 ne kawai na kudaden da CBN ya basu a bankin.
KU KARANTA KUMA Yadda Mazauna Kano Suke Bin Dogon Layi A Bankunan Kasuwanci na Jihar
A cewarta, “bama samun kudin da sauri kamar yadda muke so. Muna samun kashi 10 cikin 100 na kudaden da aka ajiye. Muna biya muna karbar kudi. Muna kuma zubawa a ATM din mu.
Mista Jimoh Garuba, wakilin bankin Sterling, ya ce yana karbar kason mako-mako daga CBN amma ba shi da isassun kudade da zai biya bukatun abokan huldar sa.
Ya ce, “yayin da muke magana, na’urarmu ta (ATM) tana rarraba abin da muka karba wanda ke canzawa mafi yawan lokaci.”
Ya ce bankin na sa ran karbar mafi karancin naira miliyan 150 daga bankin na CBN duk mako domin rabawa ga rassansa da ke Abuja.
Ya ci gaba da cewa, a Kaduna, bankin yana karbar Naira miliyan 150 duk mako wanda ake rabawa rassansa a fadin jihohi 36 na tarayya.
A cewarsa, a Kano, “muna karbar Naira miliyan 100 duk mako, kuma ta hanyar ATM ne kawai za mu iya bayarwa ba ta hanyar cikin bankin ba.
“Idan za mu bi ta kan kanta sayar da kaya don ba da kuɗin, rabon zai tafi cikin ƙasa da mintuna 10.”
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Ya ce adadin kudaden da CBN ke samu ya bambanta a kowane mako, inda ya ce yana karbar kashi 80 na abin da ya ajiye a Abuja, kuma yana samun kasa da kashi 10 a Kano.
A Wani Labarin Kuma Adeleke Ya Ki Amincewa Da Hukuncin Kotun, Zai Daukaka Kara
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke a matsayin “rashin adalci”, inda ya sha alwashin kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara.
Da yake mayar da martani kan hukuncin kotun a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Rasheed Olawale ya fitar, Gwamna Adeleke ya caccaki matakin da aka dauka na kada kuri’a a kan Mr Oyetola, inda ya kira ta “fassarar rashin adalci da akasarin masu kada kuri’a”.