Kwamishinan Kananan hukumomin Kano, Murtala Sule Garo ya musanta sauyawa makarantar koyon aikin ungozoma dake Makoda wajen zama daga inda take zuwa cikin birnin Kano.
Kwamishinan ya ce an rufe makarantar ne na wucin gadi bayan shawarar da hukumomin tsaro suka bayar ga Gwamnati, domin tabbatar da tsaron daliban.
Yace sace-sacen dalibai da ake yi daga makarantu ne dalilin mayar da karatu birnin Kano har sai an samu rahoton bude makarantar da ma wasu da aka rufe sakamakon rahotannin tsaron.
”Yanayin Tsaro ne ya Sanya dole aka koma cikin Birnin Kano da karatu, sakamakon shawarar da hukumomin Tsaro sukaa baiwa Gwamnatin Kano.” inji shi.
Ya yi alkwarin ci gaba da karatu a makarantar ta ɗanbatta nan ba da jimawa ba, wato dai idan aka samu Tsaro a Yankin dake makwantaka da makarantar.