Tsohon mataimakin Slshugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa gwamantin Buhari shaguɓe game da ƙarin farashin man fetur wanda gwamantin ta ce ya faru ne saboda janye tallafi.
Atiku ya wallafa a haka ne a shafinsa na Twitter da safiyar Talatar nan, yadda yake mamakin ƙaruwar kudin man a Najeriya alhali farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya na ta raguwa tun daga shekarar 2019.
“Ni ɗan kasuwa ne kuma ina kallon abubuwa ne ta fuskar tattalin arziƙi, ina da tambayoyi masu buƙatar amsoshi.
“Farashin ɗanyen mai ya ragu daga yadda yake a 2019 kuma a Amurka da Turai farashin mai ya ragu sosai daga yadda yake a 2019.
“Idan da gaske gwamanti ta cire hannunta, shin ba kamata ya yi a ce farashinsa ya ragu ba?
Bayannin na Atiku na zuwa ne washegarin ranar da shugaban ƙasa ya yi bayani ta bakin mataimakinsa, Yemi Osinbajo, game da abin da ya haddasa ƙarin farsashin.
Buhari ya ta’allaka ƙarin rashin da illar da annobar Korona ta yi wa tattalin arziƙi a faɗin duniya da kuma faɗuwar kuɗin ɗanyen mai.
Hakan ta sa gwamanti ta cire hannunta daga ƙayyade farashin mai, ta bari yanayin kasuwar ɗanyen mai ta yi alƙalanci.
Ya ce yanayin da aka tsinci kai a ciki ya tilasta wa gwamnati yin sauye-sauye da za a ci moriyarsu a nan gaba duk da cewa da farko ba za a ji daɗinsu ba.
Ya ce matakan sun haɗa da daina bayar da tallafin mai saboda yawan kuɗaɗen da ake kashewa a kai.
Maimakon haka za a sanya kuɗaɗen wajen a ɓangarorin ilimi da lafiya da sauran muhimman abubuwa na rayuwar ‘yan ƙasa.