Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce ba ya kullace da kowa, ya kuma yi alkawarin yin gaskiya da adalci ga dukkanin jam’iyyun siyasan da ke cikin Jihar ta Sakkwato. Ya dauki wannan alkawarin ne jim kadan da rantsar da shi a matsayin gwamnan Jihar a karo na biyu na wasu shekarun hudu, wanda mukaddashin Alkalin-alkalan Jihar, Mai Shari’a Saidu Sifawa, ya yi. A cewar shi, zai yi aiki ne tare da kowa a matsayinsa na gwamnan al’ummar Jihar baki-dayan su. Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyun hamayya da su zo su hada hannu da shi wajen ciyar da Jihar gaba. “A lokacin da muke bude wani sabon shafin, zan yi duk wata sadaukarwa wajen ciyar da Jiharmu gaba,” a tabbacin da ya bayar. Gwamnan kuma ya yi alkawarin shawo kan matsalar ruwan sha da ke addaban Jihar. A lokacin kuma da ya karanto wasu daga cikin nasaraorin da ya samu a zangon mulkinsa na farko, ya kuma yi alkawarin daukan kaddamar da wasu sabbin matakai a kan matsalar tsaro da za su kawo karshen ta’addanci a cikin Jihar. Gwamnan kuma ya ce, zai mayar da hankali ne a kan inganta harkar noma, manyan ayyuka, Ilimi da sauran sassan tattalin arzikin Jihar. “Zan yi duk abin da nake iyawa domin ganin na gaskata yardar da al’umma suka ba mu.”