A Jiya Litinin ne Shahararre kuma gawurtaccen attajirin nan na duniya Bill Gates ya sauwake wa mai dakinsa Melinda Gates bayan shafe shekara 27 ana shan soyayya.
Cikin wata sanarwa hadin gwiwa da suka fitar mutanen biyu sun ce ba su rabu don ba sa aon juna ba, sai dai wata nazari ta kashin kai.
Sanarwar wacce suka wallafa a shafin su na Tuwita, sun ce zamantakewa da su ka yi tsakanin su ta yi dadi matuƙa, to sai dai sakamakon irin sabgogi dake gaban su ya sa suka sauwake wa juna.
Shi dai Bill Gates shine ya kirkiro da Katafaren Kamfanin nan na Microsoft yayin da Melinda ke Kasancewa a matsayin Manaja.
Yanzu haka cikin wannan shekaru 27 da bakwai da suka shafe suna shan soyayya a matsayin ma’aurata, Allah Ya azurta su da samun ƴaƴan uku, kuma sun ce wannan rabuwa ba za ta hana su ci gaba da aiki tare ba.