Daga: Wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywwod Hauwa S Garba, wadda aka fi sani da Mama ta bayyana cewar ita shigowar ta harkar fim bai bata matsala ba kamar yadda sauran jarumai suke cewa sun samu a gidan su a lokacin da suka bayyana aniyar su ta shigowa cikin harkar.
Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya a lokacin da muke tambayar ta ko yaya shigowar ta harkar fim ta kasance?
Sai tace “To ni gaskiya ban samu wata matsala ba, saboda tun farko sai da na sanar da iyayena, Kuma sun nuna amincewar su akan kudurina, sannan Kuma ko da na shigo harkar ban samu wata matsala ba, Amma na ji daga Baki wasu su na fadar irin matsalar da suke samu idan sun shigo ko kafin su shigo su na samun matsala daga cikin gidan su.”
Ta ci gaba da cewar “Kuma Alhamdulillahi na dauki harkar fim a matsayin sana’a, don haka ma tun da na shigo harkar na ke samu ci gaba, babban buri na dai shi ne na gama da harkar lafiya, domin kamar yadda ban san zan shigo harkar ba, Allah yasa na samu kaina a cikin harkar ta fim, haka ban san lokacin fita ta daga cikin ta ba, sai lokacin da Allah ya yi zan fita. Fata na dai Allah ya sa mu gama da harkar lafiya. “
Daga karshe ta yi fatan alheri ga masoyan ta da Kullum su ke kara bata kwarin gwiwa.