Wata budurwa wacce bata san tana da ciki ba ta haihu jirgi na sararin samaniya. Matar mai suna Tamara ta kwashi hanya ne zata wuce Ecuador daga Madrid, Spain a jirgin KLM Royal Dutch, Legit.ng ta ruwaito.
An samu bayani kan yadda Tamara kwatsam ta hau jirgi wanda ana gab da isa Netherlands ta fara jin ciwon ciki. Sakamakon jin ciwo, Tamara ta nufi bandaki inda ta nemi yin bayan gida kawai sai haihuwa ta yi.
KU KARANTA: Zan yi aure amma da sharaɗin ba zan haihu ba saboda ‘ya’ya wahala ce a rayuwa
Kamar yadda Daily Star ta ruwaito, Tamara ta haihu ne bayan yunkurin nakuda biyu.
“Ana saura awoyi kadan kafin su sauka a Netherlands, sai ta fara jin ciwon ciki inda ta nufi bayi. Ga mamakinta, yunkuri biyu kadai tayi ta haihu,” kamar yadda kakakin asibitin Spaarne Gasthuis Haarlem Zuid ta sanar da NL Times.
Matar da dan duk suna lafiya lau kamar yadda likitoci biyu suka bayyana, bayan sun taimaka wa matar ya haihu.
Jaririn wanda aka sanya wa suna Maximiliano ya ci sunan ne bayan wani mutum wanda ya kasance da matar gabadaya lokacin.
Daga saukarsu Netherlands, an wuce da Tamara da jaririnta asibitin Spaarne Gasthuis Haarlem.
FG Ta Amince Da Fara Baiwa Ma’aikata Maza Hutun Haihuwa
Gwamnatin tarayya ta amince da fara hutun haihuwa na kwanaki 14 ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa hutun an amince da bayar da shi ne, ga mazan da matansu suka haihu.
To sai dai sanarwar ta ce mazan ma ba kowa ba, sai wanda matan su suka yi haihuwa ta farko zuwa ta huɗu.
Dokta Folasade Yemi Esan, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya (HoCSF), a ranar Litinin, a cikin wani sako mai taken ‘Kididdigar hutu bisa kwanakin aiki da amincewa da izinin haihuwa a ma’aikatun gwamnati.