Ministan Ilmi Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa shi ba shi da masaniya a fannin ilimi lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi ministan ilimi a shekarar 2015.
Malam Adamu, wanda shi ne minista mafi dadewa a kan karagar mulki, ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da aka yi da jami’ai da shugabannin hukumomin ma’aikatar a ranar Alhamis din nan.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Rusa Majalissar Kwamishinoninsa, Ya Kori Dukkan Hadimansa
Ya ce an tilasta masa yin amfani da hikima ta hanyar nada wasu farfesoshi na ilimi da sauran nagartattun hannuwa, tare da taimakon jami’an ma’aikatar ilimi ta tarayya don ba shi damar farawa da samun ci gaba.
Ministan ya yaba wa Shugaban kasar da ya ga ya cancanta kuma ya amince masa wajen dora masa irin wannan nauyi.
Adamu ya yabawa sauran mutanen da suka yi aiki tare da shi musamman Ministocin da suka yi aiki tare da shi.
Ya ce musamman Goodluck Opiah, wanda ya rike mukamin karamin minista a ma’aikatar ilimi a takaice kuma ya bayyana shi a matsayin dan uwa da suka yi aiki tare domin cimma nasarar da ake bukata a fannin ilimi.
A wani labarin kuma: Kwanaki 5 Yabar Ofis: Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Asusun Bunkasa Noma Na Kasa
Kwanaki biyar kafin barinsa ofis shugaba Buhari yayi wani sabon nadi.
Shugaba Buhari ya amince da nadin Garzali Muhammed Abubakar a matsayin babban sakataren asusun bunkasa noma na kasa.
Buhari ya nada akalla mutane bakwai a ofishin shugaban da mambobin kwamitin kungiyar.