Wata mata ‘yar Bulgaria wacce ake zargin ta fi kowa girman lebe a duniya ta ce tana da burin kara girman labbanta, amma a wannan karon kumatunta take son kara wa girma, nypost.com ta ruwaito.
Andrea Ivanovo ta bayyana cewa an yi mata ayyuka daban-daban guda 32, wanda ta kashe kusan $9,000, duk don ta zama kamar ‘yar beben Bratz, ta ce bata da shirin dena kara girman labbanta.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta fara tallafa wa direbobi mata don ƙarfafa sana’arsu
Matar mai shekaru 25 ta bayyana a shafinta na Instagram cewa tana shirin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwarta tare da kara girman kumatunta.
“Watan da ya gabata ne ranar haihuwata ta zagayo kuma na kara girman habata,” a cewarta.
“Yayin da nake yin wannan, tabbas ina so in ci gaba da kara girman labba na. Kuma ina matukar kaunarsu kasancewar na fi kowa girman labba a duniya,” inji ta.
Ya fara gyare-gyaren jiki ne a shekarar 2018 inda aka dinga yi mata allurai a duk makwanni biyu inda ko wacce allura ta kai $285.
Likitoci sun ja kunnenta a kan sanya rayuwarta cikin hadari amma duk da haka ta ci gaba da yi.
2023: Aisha Buhari Ta Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Tinubu Bangaren Mata
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da su kara kaimi wajen tabbatar da nasarar Tinubu da Shettima na takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Misis Aisha Buhari na magana ne a ranar Alhamis lokacin da ta kaddamar da kungiyar Mata da Matasan APC na kungiyar yakin neman zaben Tinubu da Shettima a Ilorin, jihar Kwara.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Ta bayyana cewa jam’iyyar ta gudanar da yakin neman zabe na musamman a lokacin yakin neman zabe na 2015 da 2019 kuma ta kuduri aniyar yin hakan tare da tabbatar da samun nasara a zabe mai zuwa.