Ban taya murna ba, babu ruwana da rikicinku na APC a Kano, Shugaba Buhari ya karyata Dan Zago.
A wani sakon kar ta kwana, fadar shugaban kasa tayi watsi da jawabin wani jigon jam’iyyar APC a Kano
Fadar shugaban kasa ta ce babu ruwan Buhari da rikicin APC Kano tun da lamarin na gaban kuliya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sakataren Gwamnatin Tarayya Ya Bukaci ‘Yan Nigeria Da Su Nisanci Yin Tafiyar Da Ba Ta Dace Ba
Hakazalika ta yi watsi da maganar da Dan Zago yai wanda yace Shugaba Buhari ya nuna goyon bayansa kuma ya tayashi murna.
Fadar Shugaban kasa ta yi fashin baki game da ikirarin da wasu yan siyasa a jihar Kano ke yi na cewa Shugaba Muhammadu Buhari na marawa wani tsagin baya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya barranta maigidansa daga maganar marawa wani tsagi baya.
Ya bayyana hakan a jawabin kar ta kwana da ya saki da daren Asabar, 25 ga Disamba, 2021.
Za ku tuna cewa jam’iyyar All Progressives Congress APC ta rabe biyu a jihar Kano ana gab da gudanar zaben shugabannin jam’yyyar na jihar.
Yayinda Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ke goyon bayan tsagi guda, Tsohon Gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau ke jagorantar dayan tsagin.
Malam Garba Shehu yace: “Fadar Shugaban kasa na watsi da jawabin da wani sagin APC a Kano ya saki cewa Shugaba Muhammadu Buhari na goyon bayansu.”
“Wannan karya ne. Hakan ba zai yiwu ba kasancewar ana zama a kotu. Shugaba Buhari bai marawa kowa baya ba.”