Suna na Miranda, ni musulma ce na san Addinin Musulunci kuma na shige shi a shekarar 2001, ni yar Texas, dake kasar USA, ni Ina cikin Addinin Krista ne a tsawon rayuwa ta, ban san lokacin dana shiga Addinin Musulunci ba na daura damarar nunawa duniya cewar Addinin MusuIunci Addinine abun gudu karshe na ganni a cikin shi dumu dumu.
Wato ni Miranda, na tashi a ciki gida ne mai rike da Akida mafi girma a bangaren Addinin Kiristanci, lokacin ina Yar kimanin shekaru 14 ina zaune ina kallon Labari a talabijin sai naga wata mata tana Kuka tana baiwa mai daukar rahoto labarin cewar an kashe Mijin ta kuma Addinin Musulunci Addini ne Wanda ya kawo zaman lafiya a duniya baki daya, na tausayawa Matar sosai hakan yasa na tambayi Iyaye na game da Addinin Musulunci sai suka ce Matar mayaudariya ce babu wani abun kirki a Addinin Musulunci hasalima Addini ne marar kyau abun kyama ga karya.
Tun daga lokacin na tsani Addinin tare da shan Alwashin ganin na nunawa duniya illar addinin, wata rana a makarantar mu sai aka bamu dama muyi rubutu game da ko wane irin addini wasu suka dauki addinai da dama ni kuma na zabi Musulunci don in yi rubutun suka don Al’umma su guji Addinin, to babu inda zan iya samu cikakken bayani game da Musulunci sai a yanar gizo kuma an gaya mun cewar lallai bazan sami labarin yadda aka sami Musulunci ba sai na yi bincike a Alkur’ani da kuma wani littafi na kusa da shi mai suna Hadisi, na yi bincike sosai a yanar gizo cikin Alkura’ani da Hadisi na kasa samun Hujja koda kwara daya da zan iya suka da nuna Musulunci munmunan Addini ne na kwashi tsawon kwanaki a kan haka kai sai dai na hakura.
Jaridar Dimokuradiyya
Lokacin da nake cika shekaru 15, nayi wani mafarki mai razanarwa ina daga kwance cikin mazanancin Bacci sai wani farin mutun da Fararan kaya a kan Doki yake mun magana daga cikin maganganun shi, bayan na farka daga bacci wata kalma kawai nake iya tunawa wacce ya dunga maimaita mun ita ce “ALLAH”, bisa dogaro da haka sai na tsunduma bincikar maanar wannan kalmar a kafar YouTube da wasu bangarori a Yana karshe kawai sai na kuma gani na a ciki Alkur’ani da Hadisi ta cikin yanar gizo.
Tun daga lokacin na fara sake sake na shiga dimuwa sosai, a takaice da kawai na karbi kalmar shahada na gane Addinin Musulunci shine Addinin gaskiya, yanzu haka ina mai shekaru 20 a duniya.
Allahu Akbar yadda na karbi Musulunci kenan.
Jaridar Dimokuradiyya