Rusashshen Shugaban Jam’iyar APC ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Abdullahi Abbas ya ce shi jami’an tsaro ba su kama shi ba.
A makon nan ne dai a ke ta raɗe-raɗin cewa Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa ta cafke Abbas ta kuma wuce shalkwatar ta da shi a Abuja sakamakon wasu kalamai da a ka ce ya yi a kan hukuncin da kotu ta yi na rusa shugabacin sa.
A wancan makon da ya gabata ne dai wata babbar kotu a Abuja ta rusa shugabacin Abbas ɗin, sannan ta tabbatar da shugabacin jam’iyar ga Ahmadu Ɗanzago, wanda ya ke ɓangaren tsohon gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau.
KARANTA WANNAN LABARIN: Har Yanzu ‘Yan Fim Basu San Ciwon Kan Su Ba – Abdulkareem Muhammad
Da ya ke shaidawa manema labarai a Kano a ranar Alhamis, Abbas ya ƙaryata rahotannin da ya ke yawo cewa wai an kama shi an kai shi Abuja.
Abbas ya shaidawa manema labarai cewa ko gaiyatar shi ƴan sanda ba su yi ba ballantana kamawa, in da ya ce kawai dai ya je Abuja ne domin maganar ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da kotu ta yanke.
Ya ƙara da cewa”Ni ya za a yi a kama ni bayan ban yi abin kunya ba, ban ci kuɗin makamai ba, ban kuma ce ni ina sama a ka raba kuɗin ba?” inda hakan ya zama shaguɓe ga Shekarau, wanda a ke zargi da hannu a wasu kuɗaɗe da su ka yi ɓatan-dabo.
“In ma kamani a kai meye abin kunya? Ai abin kunya shi ne a kama ɗan siyasa ya ci kuɗin makamai, ko kuɗi gwamnati. Ai ba abin kunya ba ne don an kama ɗan siyasa a kan rigimar siyasa. Ni maganar shari’ar nan ce ta kai ni Abuja kuma in sha Allahu mu ne da nasara. Uwar jam’iya ta riga ta ce ni ta sani a shugabancin jam’iya na jiha,”
“Hukuncin kotun ba ni ya shafa ba, saboda su da su ka tashi kai ƙara, ƙara su ka kai a kan zaɓukan mazaɓu da na ƙananan hukumomi, ba na jiha ba. Shima ɗin mun ɗaukaka ƙara kuma mu ne da nasara da yardar Allah,” in ji Abbas.
Abbas ya ƙara da cewa shi dai daga yanzu, a ƙarƙashin jagorancin sa, an daina baiwa mutum takara sama-ta-ka, dole sai an bi ƙa’idar dimokuraɗiyya sannan, inda hakan ma ya zama shaguɓe ga Shekarau.