Hakimin Zip a Jihar Taraba, Alhaji Uba, ya ce ba za su iya biyan kudin fansan Naira miliyan 120 da wadanda suka yi garkuwa da dansa da wasu mutane shida suka nema ba.
Sarkin ya shaida wa Majiyar Jaridar Dimokuradiyya hakan ne a wata hira da aka yi da shi cewa an sace dansa Buhari da wasu mutane shida a kauyen Illela da ke karamar hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba makonni biyu da suka wuce.
Ya ce masu garkuwa da mutanen na neman Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa ga kowane mutum bakwai da aka sace.
Ya Kuma kara da cewa, ya roki masu garkuwa da mutanen ne a wata tattaunawa da suka yi amma sun dage cewa sai an biya Naira miliyan 30 ga kowane mutum bakwai da suka sace.
Sarkin ya ci gaba da cewa ba zai iya biyan Koda rabin miliyan ba balle Naira miliyan 30 yayin da wasu iyayen wasu da aka sace ba su iya biyan ko da Naira 10,000.
Kazalika ya bayyana cewa shugaban masu garkuwa da mutanen ya ci zarafinsa, lokacin da yake tattaunawa don ganin an sako dansa da wasu mutane shida wadanda dukkaninsu talakawa ne.
“Shugaban Yan bindigan ya ci zarafina da yawa lokacin da na gaya masa cewa ba za mu iya biyan abin da yake bukata ba har ma ya yi barazanar zuwa fada na ya sace ni,” in ji shi.
Alhaji Uba ya bayyana cewa suna fuskantar barazanar ‘yan fashi daji da ke ko’ina a yankinsa.
“Ni kaina, ‘yan uwana da kuma jama’ata na cikin fargabar abin da ba a sani ba saboda kasancewar ‘yan bindiga da ke tafiya cikin walwala da makamansu a cikin dajin da ke kewaye da yankinmu,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da sace mutane 11 da suka hada da dan sarkin gargajiyar yankin.