An tsinci gawawwakin yara biyu a baraguzan bandaki da ya ruguje na makarantar firamare ta UK Bello Memorial da ke Paiko a karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja.
Har yanzu wakilin Jaridar Daily Trust bai gano abin da yaran ke yi a kusa da ginin da aka ce ya rufta ba.
Wasu majiyoyi sun ce yaran da suka hada da namiji da mace, suna cikin shawagi tare da abokansu a kusa da makarantar, inda ginin ya rufta musu.
Kana Kuma Nan take a karuwaito cewa Mutum biyu mutu.
A wani labarin Kuma na daban
Ƙasar Saudiya ta ƙaddamar da manhajar neman bizar Hajji da Ummara Ta wayar salula
Saudi Arabiya ta ƙaddamar da wata manhaja ta neman bizar Hajji da Ummara ta wayar salula a Birtaniya.
Saudiya ce ƙasa ta farko a duniya da ta ƙirƙiro da hanyar yin rijistar biza ta wayar salula.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta Daily Nigerian ta gano cewa sabuwar manhajar za ta baiwa maniyyaci dama ya shigar da duk bayanansa da hotuna, ya kuma ajiye sau kafin ya je ofishin buga bizar domin karɓo wa.
Sai dai kuma dole ne bayanan da maniyyaci ya bayar a manhajar ya kasance ya yi daidai da wanda zai kai ofishin buga bizar.
An kirkiro da wannan sabuwar hanyar domin saukaka hanyoyin kula da boda a Birtaniya.
Tun a bara ne dai Ministan Harkokin Waje na Saudiya, Faisal bin Farhan ya ƙaddamar da manhajar bisa umarnin Yarima Muhammad Bin Salman.
Manhajar kuma ta samu ne da haɗin gwiwar hukumomi da dama na harkokin Hajji da Ummara a Saudiya.