Daga: Wakilin Dimokaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Wata Sabuwar jaruma a Masana’antar shirya finafinai ta kannywwod, Farida Abdullahi, ta bayyana kudirin ta na fadakar da Al’umma ta hanyar fim ne ya sa ta shigo cikin Masarautar Kannywwod.
Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya, a matsayin ta na Sabuwar jaruma.
Tun da farko ta fada mana asalin ta da Kuma shekarun ta kamar haka.
“Suna na Farida Abdullahi Kuma ni haifaffiyar Sokoto ce a yanzu Ina da shekaru 23 a duniya, na yi makarantar Firamare da sakandare daga nan na tsaya. Kuma na shigo harkar fim ne kamar watanni 6 da suka gabata, zuwa yanzu na yi finafinai sun Kai guda Goma”.
Dangane da burin da take da shi a game da harkar fim kuwa cewa ta yi.
“Burin daya shigo da ni Masana’antar fim dai shi ne don na fadakar da mutane, Kuma na ji dadi sosai da Allah ya sa na samu kaina a cikin harkar.”
Mun tambaye ta ko ta fuskanci matsala a matsayin ta na Sabuwar Jaruma ?
Sai tace “To ai ka san duk wata harkar rayuwar duniya da za a yi ta, ba za a ce babu matsala a cikin ta ba, sai dai a daure don a samu a cimma nasarar abunda da ake da bukata.”
Daga karshe ta yi fatan Allah yasa ta gama da harkar lafiya.
Comments 1