By Abbas Yakubu Yaura
Bankin Duniya ya kakabawa kamfanin SoftTech IT Solutions and Services Ltd, dake samar da hanyoyin sadarwa na zamani na Najeriya takunkumi, da Manajan Daraktansa, Mista Isah Kantigi, bisa zargin cin hanci da rashawa.
DUBA WANNAN LABARIN: Ministan sufuri Amaechi, El-Rufai Suna Son Akafa Sansanin Sojoji A Rijana Da Katari
Kamfanin, wanda ke da hannu a cikin Tsarin Tsaron Zaman Lafiyar Jama’a, an sanya masa takunkumi na tsawon watanni 50 yayin da aka sanya wa manajan darakta takunkumi na watanni 60.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai suna ‘Kungiyoyin Bankin Duniya sun hana kamfanin SoftTech IT Solutions and Services Ltd. da manajan daraktan sa’, wanda aka buga a gidan yanar gizon bankin a ranar Laraba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kungiyar Bankin Duniya a yau sun sanar da dakatar da kamfanin SoftTech IT Solutions and Services Ltd., wani kamfanin samar da hanyoyin sadarwa na zamani da ke Najeriya, na tsawon watanni 50, tare da dakatar da manajan darakta na tsawon watanni 60.
Inda suka ce dan gane da ayyukan cin hanci da rashawa a matsayin wani bangare na aikin tsaron lafiya na kasa a Najeriya.
“Tsarin da aka yi ya sa SoftTech da Mista Isah Kantigi, dan Najeriya, ba su cancanci shiga ayyukan da Bankin Duniya ke bayarwa ba.”
Bankin Duniya ya ce an sanya wa kamfanin da manajan darakta takunkumi saboda biyan wasu jami’an ayyukan da ba su dace ba.