Bankin Duniya ya ware Dalar Amurka Miliyan Dari Bakwai domin aikin kawar da zaizayar kasa da noman damuna mai taken ACRESAL a Najeriya.
Shugabar shirin Dr. Joy Iganya Agene ta bayyana hakan a lokacin da ta ziyarci mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a ofishin sa.
Ta ce aikin wanda ya maye gurbin NEWMAP da aka tsara don shawo kan zaizayar kasa da fadada wuraren ban ruwa a jihohi 19 har da babban birnin tarayya Abuja zai yi tasiri a kananan hukumomin DawakinTofa, Nassarawa da Shanono a kano.
KARANTA KUMA: Bankin Duniya Ya Dakatar Da wani Kamfanin Najeriya Saboda Wani Zargi
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Dokta Joy Iganya Agene wadda ta yabawa gwamnatin jihar kano bisa amincewa da biyan takwararta tallafin kudi na Naira Miliyan Dari Biyar, ta ce bankin duniya ya gamsu kuma ya samu gagarumar nasara wajen hada hannu da kano kan kare muhalli da sauran sassa.
A nasa bangaren mataimakin gwamnan jihar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna kuma dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC ya godewa bankin duniya bisa hadin gwiwa da gwamnatin kano akan ayyukan raya kasa tare da bada tabbacin samun cikakken goyon baya domin samun sakamako mai kyau.
Tun da farko kwamishinan muhalli Dr. Kabiru Ibrahim Getso ya bayyana cewa shirin NEWMAP tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar kano ya kammala fadada aikin noman rani a karamar hukumar Tofa da ayyukan yaki da zaizayar kasa a sassa daban daban na jihar. COV/NBA
A Wani Labarin Kuma: Wani Hadarin Mota Ya Yi Sanadin Rayuka 5, Ya Raunata 3 A Kogi
Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan wasu uku suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a Kogi ranar Lahadi, kamar yadda Mista Stephen Dawulung, Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC) na jihar Kogi ya bayyana.
Dawulung, wanda ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici matuka,” ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a Lokoja a ranar Lahadin nan cewa hadarin mota ya faru ne a mahadar Ogbagbo da ke kan hanyar Ejule zuwa Ochadamu da misalin karfe 12.47 na rana. lokacin da wata mota kirar Nissan ta yi karo da wata motar Mazda.