Kungiyar Bankin duniya, IDA ya ce zai bai wa kasar Benin Dala miliyan 60 a wani mataki na taimakon kasashen Afrika maso yamma su yi aiki da rashin aikin yi a tsakanin matasa. Kamar yadda sanarwar da Bankin ya fitar a ranar Talata a garin Kwatano ya nuna.
Bankin ya ce sun yi hakan domin ganin sun taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar sanya matasa da suke fama da talauci wajen bas u ayyukan yi da kuma horo na musamman.
Matasan da ake sa ran za su amfana da wannan tallafin sun hada daga ‘yan shekaru 15 zuwa 30, wanda Bankin ya ce kashi 50 na tallafin za a tallafawa mata ne da ba sa zuwa makaranta.