Bankin Jaiz Plc, babban bankin Musuluncin da ba riba a Nijeriya, a jiya ne aka ba da sanarwar cewa shi ne Babban Bankin Musulunci da ke ci gaba a shekarar 2021 kuma mafi inganci a duniya inda ya lashe lambar yabon Bankin Musulunci na duniya (GIFA).
Shugaban GIFA, Farfesa Humayon Dar, ya taya Bankin Jaiz murnar lashe kyautar, inda ya ce Bankin ya kasance mafi kyawu daga cikin Bankuna uku da aka yi la’akari da su a cikin wannan rukunin bayan doguwar tattaunawa wanda aka dogara da wasu dalilai da ya haɗa da tsarin GIFA.
Hanyar GIFA wacce ake bi wajen ba da kyaututtukan, kuma ake zaɓar waɗanda suka yi nasara, ita ce hanya da ake bi wajen bincike domin duba kawai mafi cancanta a cikin nau’ikan kyaututtukan su.
A cewar kwamitin karramawar, Bankin Jaiz ya sami damar cika dukkan abubuwan da aka gindaya, don haka wannan shi ne dalilan da ya sanya ya yi nasara.