By Abbas Yakubu Yaura
Asusun ba da lamuni na duniya, IMF, a jiya yace bankunan Najeriya sun rufe rassa dari 234 da na’urorin cirar kudi ATM guda dari 649 a shekarar 2020 wanda hakan ya haifar da faduwar darajar kudin kasar zuwa naira 4.44 a shekara idan aka kwatanta da naira 4.78 a shekarar 2019.
IMF ta bayyana hakan a cikin bincikenta na samun damar Kudi na shekarar 2021 da Ci gaban da aka fitar jiya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa rahoton yace kasashen duniya na amfani da alamomi guda biyu na FAS wajen sanya ido kan manufa 8.10 na shirin ci gaba mai dorewa na shekarar 2030 (SDGs) da ke da nufin karfafa karfin cibiyoyin hada-hadar kudi na cikin gida don fadada hanyoyin yin ayyukan banki da hada-hadar kudi.
Alamomin FAS guda biyu sune Adadin rassan Bankin Kasuwanci na Manya 100,000 da Adadin ATM na Manya 100,000.
A cewar rahoton, Najeriya ta sami raguwa a cikin waɗannan mahimman bayanai na FAS guda biyu da wasu alamomi guda 12 a cikin alamomi 64 da FAS ta auna.
Sannan a cewar rahoton, ya biyo bayan raguwar rassan bankunan kasuwanci a Najeriya zuwa dubu 5,158 a shekarar 2020 daga 5,392 a shekarar 2019. Sakamakon haka, adadin rassan bankunan kasuwanci na 1,000 km2 a Najeriya ya ragu zuwa 5.94 a shekarar 2020 daga 5.68 zuwa shekarar 2019.
Haka kuma, Adadin ATMs na kowane kilomita 1,000 a Najeriya ya ragu zuwa 20.65 a shekarar 2020 daga 21.36 a shekarar 2019. Rahoton na IMF ya kuma nuna cewa an samu raguwar adadin masu karbar kudi ta wayar salula a Najeriya zuwa 129,154 a shekarar 2020 daga 145,800 a shekarar 2019. kashi 11 cikin dari sun ragu.