Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, MACBAN, ta yabawa Fadar Shugaban Kasa akan saka baki cikin batun umurnin da gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akerelodu ya bada na korar makiyaya daga dajikan da ke jiharsa.
Sakataren kungiyar na kasa, Usman Baba-Ngelzerma ya shaidawa The Punch a ranar Laraba cewa Fadar Shugaban Kasar ta fadi gaskiya a yayin da ta ce makiyayyan su cigaba da zamansu a jihar.
Da ya ke mayar da martani ya ce, “Don me zan saba umurnin shugaban kasa? Yana magana ne a madadin kasa baki daya. Yana jadadda abinda kundin tsarin mulki ne ya fada, illa iyaka. Abinda Fadar Shugaban Kasa ta fadi shine abinda ya dace. Fadar Shugaban Kasar ta jadadda abinda kundin tsarin mulki ya ce.”
Baba-Ngelzerma ya ce kawo yanzu kungiyar ta makiyaya ba ta samu wani umurni a hukumance da ke neman su fice daga jihar ba.
Ya ce a halin yanzu, makiyayan za su cigaba da zama a inda suke, ya kara da cewa suna zaune lafiya da mutanen garuruwan.