Ministan yada labarai da raya al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin abin dariya.
A wani faifan bidiyo da aka fitar a karshen mako, masu garkuwa da fasinjojin jirgin kasa a Kaduna sun yi barazanar yin garkuwa da Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna tare da kashe su.
DUBA WANNAN LABARIN: Majalisa tace da sake kan kashe Dala Biliyan 1 wajen yaki da Maleria
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron majalisar zartaswa ta tarayya da shugaba Buhari ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja, a ranar Laraba, ministan ya ce ‘yan ta’addan suna yada farfaganda ne kawai.
Dangane da Sanatoci da suka yi barazanar tsige Buhari idan har ba a magance matsalar rashin tsaro cikin makonni shida ba, Mohammed ya ce gwamnati ce kan lamarin, kuma tana yin bakin kokarin ta.
Ya ce: “Muna yin duk mai yiyuwa don tabbatar da cewa al’ummar kasar suna cikin tsaro sosai kuma lokaci ya yi da za a ga sakamako.”