Hukumar jami’an tsaron farin kaya DSS ta bukaci kungiyar malaman jami’a ta kasa ASUU da ta janye yajin aikin da take yi saboda dalilan tsaro.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da kotun da’ar ma’aikata ta baiwa kungiyar malaman jami’ar umarnin janye aiki da suka shafe watanni bakwai suna yi saboda rashin cika musu alkawarukan su da gwamnatin tarayya tayi.
Daraktan hukumar dake jihar Yobe, Yunusa Abdulkadir, ne ya bukaci hakan yayin taron shugabanin hukumomin tsaro na arewa maso gabashin kasar nan da akeyi duk bayan watanni ukun shekara a Damaturu.
KARANTA ANAN: Gwamna Ganduje Ya Bude Cibiyar Kula Da Masu Cutar Tamowa
Ya ce yajin aikin da ya durkusar da jami’o’in kasar nan na da tasiri kan sha’anin tsaro.
Yunusa Abdulkadir, y ace ya kamata kungiyar malaman jami’ar suyi na tsanaki kan kalubalan da arewa maso gabashin kasar nan ke fuskanta tsaron shekaru a sanadiyar ayyukan ‘yan bindiga.
Daraktan hukumar ya kuma bukaci da asamar da asibitin lura da masu matsalar kwakwalwa don kula da wadanda suka samu matsala a sanadiyar rashin tsaro.
Ya ce rashin yin hakan zai ta’azzara matsaloli ga wadanda abin ya shafa wanda kuma hakan wata barazana ce ga matsalar tsaro a jihar.
A wani labarin kuma: Zamfara: PDP Ta Zaɓi Ranar Sake Zaɓen Fidda Gwanin Yan Takarar Gwamna
Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara ta sanya ranar Juma’a (gobe) domin sake gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamna a jihar.
A ranar Juma’ar da ta gabata, wata babbar kotun tarayya a jihar ta soke zaben fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar da Alhaji Dauda Lawal Dare wanda ya lashe zaben fidda gwanin.
To sai dai bisa dalilin saba ka’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar na daga cikin dalilin da ya sanya kotun soke zaben, bayan tsohon dan majalisar tarayya Alhaji Ibrahim Shehu Gusau, ya roki kotu da ta soke zaben da ya ce yana cike da kura-kurai.