Kungiyoyi uku sa suka rage a sabuwar gasar zakarun turai ta European Super League wato Reala Madrid da Juventus da kuma Barcelona, sun ba gudu ba Ja da baya kan manufar su ta kirkirar gasar.
A watan da ya gabata ne sai Ƙungiyoyi 12 suka ɓullo sa sabon salon kirkiro da wannan gasa. To sai daga baya tara daa cikin su sun janye vayan da magoya bayansu suka nuna adawa a kai.
Amma a wata Sabuwar sanarwar haɗin gwiwa da Barcelona da Real Madrid da Juventus suka fitar a yau Laraba, sun ce babu gudu babu ja da baya dangane kirkirar wannan gasa.
Sun bayyana cewa ba za su zauna kawai su nade hannu ya zamo cewa kura da shan bugun gardi da kwace kudi ba tsakaninsu da Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar tura wato UEFA ba.
Da ma dai hukumar ta UEFA ta gargadi Ƙungiyoyin uku da suka rage cikin gasar da kada su kuskura su bari guri ya kure musu, domin kuwa za su yaba wa aya zakinta.
Sanarwar ta Ƙungiyoyin ukunl ta ce dole ne a yi gyarana fuska wa harkar wasanni, ko kuma su ci gaba da zura idanu tana rugujewa tunda hukumar ta UEFA ta nuna gazawarta da kum maitar kuɗi.