Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce ya gamsu da yadda mai horar da ƙungiyar Ronald Koeman ke aiki, kuma babu shirin korarsa. (Sport)
Wata majiya ta ce PSG ta nemi shiryawa da Cristiano Ronaldo kafin ya bar Juventus ya koma tsohuwar ƙungiyarsa Manchester United. (Goal)
Ɗan wasan gaban Chelsea Romelu Lukaku ya ce tsohuwar ƙungiyarsa Inter Milan ta inganta rayuwarshi a lokacin da ya bar Manchester United a 2019. (Daily Mail).
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Yan fim yan Kwankwasiyya sun ziyarci Gwamna Ganduje
Ɗan wasan gaban Liverpool Mohamed Salah mai shekaru 29 ya nemi ƙungiyar ta riƙa ba shi fam 500,000 duk mako idan har tana so ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya. (Mirror)
Damar da Tottenham take da ita ta sayen Adama Traore daga Wolves a watan Janairu ta haɗu da cikas, bayan da ɗan wasan ya fara tattauna batun ƙulla sabuwar yarjejeniya da ƙungiyarsa. (Express)
Sayen Neymar a 2017 daga Barcelona da PSG tayi zuwa yanzu ta kashe fam miliyan 489 kama daga kuɗin sayensa zuwa albashinsa. (Marca)
Tsohon ɗan wasan Bayern Munich da Faransa Franck Ribery zai koma ƙungiyar Salernitana da ke Italiya mako mai zuwa. (Fabrizio Romano)
Ƙungiyoyin Tottenham da Chelsea sun ƙyalla ido kan ɗan wasan tsakiyar Ivory Coast Franck Kessie, bayan da yaƙi amincewa da ƙulla sabuwar yarjejeniya da AC Milan. (Gazzetta dello Sport – in Italian)
Comments 1